1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba da kashe masu bore a Sudan

Binta Aliyu Zurmi
January 18, 2022

Babban jami'in harkokin ketare na Kungiyar Tarayyar Turai Josep Borrel ya ce dakarun sojin kasar Sudan sun bujire wa kiraye-kirayen hawa teburin sulhu domin kawo karshen rikicin da kasar ke ciki.

https://p.dw.com/p/45hgY
Frankreich Straßburg | Europäisches Parlament | Josep Borrell
Hoto: Alexey Vitvitsky/Sputnik/picture alliance

Wannan jawabi na babban jami'in kungiyar ta EU dai na zuwa ne kwana guda bayan da sojoji a Sudan din suka bude wa masu zanga-zanga wuta da ya kai ga kashe mutane bakwai.

Boren ya ce ci gaba da amfani da karfi wajen murkushe masu bore, da ma kame yan jarida gami da masu fafutuka na kara saka kasar a wani hali na tsaka mai wuya.

Sama da mutane 70 ne ya zuwa yanzu suka rasa rayukansu tun bayan da sojoji suka karbe madafun iko a watan Oktoban shekarar da ta gabata.