Faɗa tsakanin 'yan taliban da sojojin Afganistan
May 8, 2011Talla
Dakarun gwamnatin Afghanistan na ci gaba da fafatawa kwana na biyu a jere da 'yan taliban a birnin kandahar, bayan ƙaddamar da hare-haren ta'addaci akan gine ginen gwamnati da masu tsananin kishin addinin suka yi. Jami'an ma'aikatar cikin gidan sun bayyana cewa 'yan takifen sun yi amfani da rokoki domin aiwatar da wasu jerin hare-haren da suka halaka mutane uku, tare da jikata wasu karin 40.
Mazauna birnin Kandahar suka ce suna ji ƙarar aman bindigogi masu jigida da kuma tashin bama-bamai tun bayan da sojojin Nato suka fara mara wa dakarun gwamnati baya. Hukumar leƙen asiri na Afghanistan ta ce wannan fito na fito na daga cikin tsarin da ta tanada na sa ƙafar wando guda da taliban.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi