Kenya:'Yan majalisa sun bai wa hamta iska
December 29, 2021Talla
'Yan majalisar akalla guda biyu sun rika yin dambe a cikin zauren har sai da shugaban majalisar ya dakatar da zaman tattaunawar. Gidan talbijan na Kenya ya nuno daya daga cikin masu fadan dan majalisar da jini jina-jina a fuskarsa. Fadan ya barke ne a kan kudirin dokar da ke yin kwaskwarima wajen tsara tafiyar jam'iyyun siyasa da irin kawancen da suke iya yi. Masu adawa da kudirin na zargin cewar shugaba Uhuru Kenyatta, na iya yin amfani da kudirin domin yin kawance da tsohon abokin adawarsa Rail Odinga a zabukan gama gari da za a yi a cikin watan Augustan da ke tafe.