Fada na ci-gaba da gudana a Sudan ta Kudu
December 21, 2013Sojojin gwamnatin Sudan ta Kudu sun durfafi birnin Bor da ke arewacin Juba da nufin yinta ta kare da bangaren da ke goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasa Riek Machar. Wani kakakin kungiyar SPLM mai suna Philip Aguer ne ya yi wannan bayanin, inda ya ce suna samun gudunmawar jiragen sama masu saukar ungulu a fafatawa da suka yi da bangaren Machar.
Tun dai ranar 15 ga wannan wata na Disemba ne fada ya barke tsakanin bangaren shugaban kasa Salva Kiir da kuma na tsohon mataimakinsa Riek Machar da ke neman hambarar da gwamnatinsa. Tuni dai kasar Kenya ta tura da dakaru Sudan ta Kudu domin kwaso 'ya'yanta da ke da zama a wannan kasa.
Majalisar Dinkin Duniya da kuma kasar Amirka sun yi kira ga bangarorin da ke gaba da juna da su zauna kan teburin shawarwari domin dinke barakar da ke tsakaninsu. Fadar mulki ta Washington ta yi gargadin katse tallafin da take bai wa Sudan ta Kudu idan ta ci-gaba da yin kunne kashi da kiraye-kirayen da ake yi mata na kai hankali nesa.
Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Mohammad Nasiru Awal