1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ba ta kashi a kan iyakar Isra'ila da Gaza

Abdul-raheem Hassan MNA
May 14, 2018

Akalla Falasdinawa 40 sun mutu yayin da kimanin mutane 400 suka jikkata yayin wata arangama tsakanin masu zanga-zanga da 'yan sanda a kan iyakar Zirin Gaza da Isra'ila.

https://p.dw.com/p/2xgva
Proteste im Gazastreifen an der Grenze zu Israel
Hoto: Reuters/M. Salem

A wata sanarwa da rundunar sojojin Isra'ila ta fitar na cewa sojojin sun bude wuta kan masu boren a wani mataki na mai da martani don kare kai daga farmakin Falasdinawa masu zanga-zanagar.

Artabu tsakanin jami'an tsaron Isra'ila da Falasdinawan ya barke ne bayan wata zanga-zangar da aka kiyasta Falasdinawa dubu 35,000 ke yi a yankin Zirin Gaza, dab da lokacin da Amirka ke shirin bude sabon ofishin jakadancinta a Birnin Kudus.

A wannan Litinin Amirka ta bude sabon ofishin jakadancinta bayan wani biki a Birnin Kudus, duk da adawa da wannan matakin da kasashen duniya suka nunha.