Fada ya kazance a Sudan
May 16, 2023Talla
Ana ci gaba da fafata fada da mayan makamai gami da jiragen saman yaki a birnin Khartoum fadar gwamnatin kasar Sudan tsakanin sojoji da rundanar mayar da martani, kamar yadda mazauna birnin suka tabbatar, inda aka kwashe kimanin wata guda ana tashin hankali. Kusan mutane 700 suka halaka yayin da wasu fiye da 5,500 suka jikata kuma harkokin jinkai suka tabarbare.
Kungiyoyin kula da agaji sun bayyana cewa kimanin mutane milyan tara suke rayuwa kusa sa inda ake fafata wannan fada.
Tuni babban habsan sojan kana shugaban gwamnatin wucin gadi, Janar Abdel Fattah Burhan ya saka hannu kan ayar dokar rufe asusun ajiya na banki na daukacin rundunar mayar da martanin.