Fadan taho mu gama a Senegal
November 21, 2007Talla
Jami´an ´Yan sanda a Senegal sun harba barkonon tsohuwa cikin gungun masu zanga-zangar adawa da Gwamnati. Faɗan taho mu gaman tsakanin ɓangarorin biyu ya farune, bayan Gwamnati ta Umarci tashin masu saye da sayarwa, a bakin titunan babban birnin ƙasar ne wato Dakar. Rahotanni sun shaidar da cewa masu zanga zangar sun daddatse manya manyan hanyoyin birnin na Dakar tare da ƙone-ƙonen tayoyi. Hakan dai a cewar bayanai ya kawo tsaiko, a harkokin zirga zirgar sufuri a birnin na Dakar. A yanzu haka dai Jami´an ´ Yan sandan na ƙokarin shawo kan wannan al´amari.