Fafaroma Francis: A yi hattara da batun birnin Kudus
December 6, 2017Talla
Fafaroman wanda ya bayyana haka daf da lokacin da shugaban Amirka Donald Trump ke shirin bayyana birnin na Kudus a matasayin babban birnin Isra'ila. Ya ce birnin Kudus shi ka dai shi ke, birnin na Yahudawa da Musulmi da kuma Kirista wadanda ko wane ke bauta wa addininsa. MDD da China da Birtaniya sun bayyana fargabansu a game da matakin da shugaban Amirka yake shirin dauka.