1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafutukar kwace garin Kobani

October 13, 2014

Mayakan Kurdawa na ci gaba da fuskantar tirjiya daga 'yan kungiyar IS, a kokarin da suke na fatattakar su daga garin Kobani da ke kan iyakar kasashen Siriya da Turkiya.

https://p.dw.com/p/1DU1l
Hoto: REUTERS/U. Bektas

Rahotanni na nuni da cewa Kurdawan na samun galaba a kan 'yan kungiyar ta IS duk kuwa da cewar mayakan na IS na ci gaba da harba rokoki zuwa tsakiyar garin na Kobani. Kungiyar kare hakkin dan Adam da ke sanya idanu a yakin na Siriya ta ruwaito cewa akallah mayakan IS 36 ne suka sheka barzahu a 'yan kwanakin nan, kuma baki dayansu 'yan kasashen ketare ne da suka je Siriya domin taimakawa wajen sauke gwamnatin Shugaba Bashar al-Asssad na Siriya.

Yayin da a hannu guda kuma mayakan Kurdawa takwas suka hallaka a fafatarwar da suke da 'yan IS din. Wannan dai na zuwa ne duk da yakin taron dangi da Amirka ke jagoranta a kasashen Siriya da Iraki domin kawo karshen ayyukan 'yan ta'addan na IS.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Suleiman Babayo