Fafutukar yaki da ta'addanci a duniya
December 14, 2017Talla
Sakamakon sanarwar da aka bayyana ta samun karuwar ayyuka tarzoma, kasashen duniya daba-daban sun tashi tsaye haikan wajen yaki da ta'addancin wanda ke ci gaba da samun gindi zama a duniya. Yayin da kungiyar IS ke kara tayar da tarzoma a Siriya da Iraki, tare da kai hare-hare a wasu sassa na duniya, ita kuma Boko Haram da masu jihadi na Mali sun addabi kasashen yankin yammacin Afirka.