Gaza: Shekara guda da dawowar fafutuka
March 30, 2019Talla
An dai ci gaba da zanga-zanga duk mako a fafutukar da Falasdinawa suka sanya a gabansu, ta ganin an dawo masu da yankunan da Isra'ila ta mamaye wadanda ke zama wuraren da iyaye da kakannin Falasdinawan suka zauna, da ma fafutukar ganin an kawo karshen shekaru goma sha biyu na rufe iyakarsu da Isra'ila ta yi.
A wannan Asabar dai ana sa rai na ganin yawan jama'a da za su fita yayin da a bangare guda kuma Falasdinawan ke kiran gudanar da maci na mutane miliyan guda ba kawai a yankin na Falasdinawa ba har da sauran kasashen Larabawa da kasashen Turai.