A daidai lokacin da Amirka ke gudanar da shagulgulan bude ofishin jakadancinta a kasar Isra'ila a birnin Kudus, dakarun sojin Isra'ila sun bindige gwamman Falalsdinawa a yankin Gaza, a yayin da suke kokkarin kutsawa yankunansu da Isra'ila ta mamayae tun shekaru 70 da suka gabata.