1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Falasdinawa sun mutu a farmakin Isra'ila

Mouhamadou Awal Balarabe
October 25, 2022

Wani farmakin da sojojin Isra'ila suka kai a Gabas Yamma da kogin Jordan ya haddasa mutuwar Falasdinawa shida , a lokacin da ake neman gungun matasa da ke da hannu wajen kai hare-hare ruwa a jallo.

https://p.dw.com/p/4IfvO
Westjordanland | Militäreinsatz Israels in Nablus
Hoto: Raneen Sawafta/REUTERS

Cikin wata sanarwar da ta fitar, rundunar sojan Isra'ila ta ce Falasdinawa da dama sun kona tayoyi tare da jifar sojoji da duwatsu, lamarin da ya sa su mayar da martani ta hanyar bude wuta.

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya yi Allah wadai da harin tare da danganta shi da laifi na yaki. Yayin da a nasa bangare, firaminista Isra'ila Yair Lapid ya ce mataki ne na rage ta'addanci da tabbatar da cewa hakan bai shafi 'yan kasar Isra'ila ba.

Tashe-tashen hankula sun karu a 'yan watannin baya-bayannan a arewacin gabar yammacin kogin Jordan, inda sojojin Isra'ila suka kara kaimi sakamakon munanan hare-haren kin jinin Isra'ila, wadanda suka yi sanadin mutuwar mutane fiye da Falasdinawa 100 a cewar MDD.