Falasdinawa sun samu nasara a MDD
September 11, 2015Talla
Kasashe 119 suka kada kuri'ar amincewa Falasdinawan, su kafa tutuar tasu, yayinda kasashe bakwai kacal suka jefa kuri'ar kin amincewa, ciki kuwa harda Isra'ila da Amirka. A yanzu hakan 'yankin Falasdinu da fadar Vatikan, sune kadai kasashen da ke da tuta na 'yan kallo da ba cikakkakun mambobi a majalisar. A ranar 30 ga watan da muke ciki ne shugaban Falsdinawa Mahmud Abbas, zai daga tutar Falasdinawan a MDD bayan jawabin da zai yi wa zauren. Isra'ila dai ta soki matakin da aka dauka na barin Falsdinawa su kafafa tuta, domin hakan ya nuna duniya na kan hanya da basu yanci a matsayin kasa baki daya, inda tuni a yanzu Falasdinawa ke da kujera a UNESCO da kotun MDD da ke hukunta manyan laifuka a birnin Hague.