Isra'ila za ta yi amfani da iko don karin gabar kogin Yamma
September 10, 2019Talla
Tun da farko sai da duk da cewar Firaiminsta Mohammed Shtayyeh na Falasdinu ya gargade Netanyahu tare da jan hankalinsa kan ya guji yada manufofin siyasa ta hanyar amfani da yankunan kasar Falasdinawa.
Cikin shekaru gomman da Firaiminstan Netanyahu ya kwashe yana mulkin kasar wannan ne karo na farko da ya jajjirce wajen shigar da wani yanki Isra'ila.
Dubunnan Yahudawa sun yi sansani a gabar kogin Yamman tun 1967 koda yake har ya zuwa wannan lokaci Falasdinawa na ikirarin mallakinsu ne.
Al'ummar Falsadinu sun yi Allah wadai da wannan alwashi na Netanyahu tare da zarginsa da rusa shirin sulhunta yankunan biyu ta hanyar fakewa da yada manufofin siyasa.