1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe Falasdinawa saboda daba wuka

Yusuf BalaOctober 17, 2015

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi wani zama na gaggawa kan wannan rikici da ya lakume rayukan mutane da dama.

https://p.dw.com/p/1GpoA
Israel Anschlag in Jerusalem
Hoto: Reuters/R. Zvulun

An halaka wasu Falasdinawa uku ta hanyar amfani da bindiga bayan da suka yunkara wajen daba wuka ga wasu 'yan Isra'ila a Gabashin Jerussalam da yamma da kogin Jodan a ranar Asabar. Rikicin da ke faruwa a wannan yanki dai na ci gaba da sanya fargabar barkewar rikici tsakanin bangarorin biyu da aka dade ba a ga miciji da juna.

Bayan makonni biyu ana ta arangama da ta yi sanadin rayukan mutane da dama a ranar Juma'a shugaba Obama ya bukaci dukkanin bangarorin biyu su mai da wukakensu kube a yayin da a bangare guda kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi wani zama na gaggawa kan wannan rikici.

Ya zuwa yanzu dai wannan rikici ya yi sanadin lakume rayukan Falasdinawa 40 yayin da a bangaren Isra'ila ta rasa mutanenta bakwai, tun bayan rikicin da aka fara a ranar daya ga watan nan na Oktoba.