Falasdinu ta kira wasu jakadunta su dawo
May 16, 2018Talla
Kasashen hudu dai sun ware daga cikin tawagar manyan kasashen Turai wadanda suka ki aikewa da wakilansu a ranar lahadin da ta gabata yayin bikin tarbar wakilan Amirka don bude Ofishin Jakadancinta da aka gudanar a ranar Litinin.
Kungiyar Tarayyar Turai ta soki ayyana birnin na Kudus da shugaba Donald Trump yayi a matsayin babban birnin kasar Isra'ila tare kuma da mayar da ofishin jakadancin Amirkar zuwa birnin na Kudus.