1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Falesdinawa na neman kai Isra'ila kara

August 5, 2014

Ministan harkokin wajen Falesdinu ya yi tattaki zuwa kotun kasa da kasa da ke The Hague domin duba yiwuwar kai Isra'ila kara a kan kashe-kashen da ta yi a Zirin Gaza.

https://p.dw.com/p/1CpIb
Hoto: Reuters

Ministan harkokin wajen Falesdinu Ryad al-Maliki ya jadadda aniyar yankinsu na shigar da kara gaban kotun hukunta manyan laifukan yaki da ke birnin The Hague, domin ta hukunta Isra'ila a kan kashe-kashen fararen hula da ta yi a Zirin gaza.

Minista al-Maliki ya gana da babbar mai shigar da kara a kotun Fatou Bensuda domin tattanawa kan hanyoyin da za a bi wajen samar wa Falesdinu kujera a cikinta. Wannan matakin ne dai zai iya share wa kotun ta kasa da kasa fagen sauraran karar da Falesdinu za ta shigar kan rikicin yankin Gabas ta Tsakiya. Matsayin 'yar kallo da majalisar Dinkin Duniya ta bai wa Falesdinu ya na bata damar shiga manyan hukumomi na duniya

Ita dai Isra'ila ta yi ta kai hare-hare ta sama da kuma ta kasa a zirin gaza da nufin murkushe kungiyar Hamas. Yayin da ita kuwa kungiyar ta yi ta harba wa Isra'ila rokoki. Sai dai kuma yanzu haka sassa biyu na girmama yarjejeniyar tsagaita wuta ta tsawon sa'o'i 72 wadda ta bayar da damar gudanar da ayyukan jinkai a yankin Zirin Gaza.

Falasdinwa kusan 2000 ne suka rasa rayukansu a wannan rikici yayin da a bangaren Isra'ila kuwa aka samu asarar rayukan soje da fararen hula 60.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Mohammad Nasiru Awal