Falesdinu zata mika wani kudri ga MDD
December 17, 2014Talla
A ranar Talata ce dai (16.12.2014) mai baiwa shugaban Falesdinawa Mahmoud Abbas shawara Nimr Hammad, ya tabbatar da wannan batu a Ramalla da ke yankin Kogin Jordan, sai dai kuma daya daga cikin jagororin na Falesdinawa a Majalisar Dinkin Duniya, ya sanar cewa a safiyar wannan Larabara ce, za su samu wani zama da wakillan kasashen Larabawa membobi a majalisar domin samun tabbacin goyon bayansu kafin a kai ga mahawara kan wannan batu nan da 'yan kwanaki masu zuwa.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu