Fara aikin da shirin zaman lafiya na Sudan ta Kudu
October 26, 2015Talla
Gwamnatin Sudan ta Kudu da bangaren 'yan tawaye sun fara aiwatar da matakan zaman lafiya. Gwamnatin ta ce a wannan Litinin an fara aiwatar da tsaro da ke cikin yarjejeniyar da ta kulla da 'yan tawaye, abin da zai bude hanyar aiwatar da ita baki daya.
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Peter Bashir Mandi ya ce an fara aiki da shirin sake hade sojoji daga duk bangarorin. Kasar ta Sudan ta Kudu ta fada cikin yakin basasa a watan Disamba na shekara ta 2013 lokacin da Shugaba Salva Kiir ya zargi tsohon mataimakinsa Riek Machar da yunkurin kifar da gwamnati, lamarin da ya kai ga mutuwar dubban mutane yayin da wasu masu yawa suka tsere daga gidajensu.