1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiLebanon

Lebanon: 'Yan gudun hijira na komawa

December 12, 2024

Wasu daga cikin 'yan Lebanon da suka tsere daga yankunan da suke fama da hare-haren a kudancin kasar, sun fara komawa gida.

https://p.dw.com/p/4o4yI
Gabas ta Tsakiya | Rikici,Lebanon | Hezbollah | Isra'ila | Gina Kasa
Mutanen da dama ne dai suka tsere sakamakon rikicin Isra'ila da Hezbollah a LebanonHoto: Mahmoud Zayyat/AFP

Masu komawa gidan dai na ta lissafin irin dimbin asarar da suka tafka daga rikicin Isra'ilar da kungiyar Hezbollah da aka kawo karshensa a baya-bayan nan, inda aka yi kiyasin an yi asarar biliyoyin daloli. A ranar 27 ga watan Nuwambar da ya gabata ne, aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a rikicin da aka kwashe tsawon watanni ana barin wuta a kudancin Lebanon din. Yakin Isra'ila da kungiyar Hezbollah a kudancin Lebanon din dai, ya yi sanadin salwantar rayukan kusan mutane 400 wasu sama da dubu 16 kuma suka jikkata kamar yadda ma'aikatar lafiya ta kasar ta sanar. A hannu guda kuma mutane fiye da miliyan guda ne suka rasa muhalli sakamakon wannan rikici, yayin kuma da harkokin tattalin arziki ya shiga mawuyacin hali. Kimanin kaso 60 cikin 100 na manoma a kudancin Lebanon, ba su samu damar kwashe amfanin gonar da suka noma a bana ba saboda yakin. Rose Bechara da ta assasa wani kamfani na sarrafa man zaitun a yankin Deir Mimas na daga cikin wadanda suka tafka asara mai yawa, inda aka yi kiyasin ta rasa kudin da ya kai dalar Amurka dubu 500 musamman ta fuskacin na'urorin da kamfanin ke amfani da su.

Gabas ta Tsakiya | Rikici,Lebanon | Hezbollah | Isra'ila | Gina Kasa
An yi asarar dukiya mai yawa a Lebanon, saboda rikicin Isra'ila da kungiyar HezbollahHoto: ELIE BEKHAZI/ABAAD/AFP

Kafin yanzun ma dai kasar na cikin yanayi na tawayar tattalin arziki, bayan halin na koma-baya da ta shiga a 2019. Faduwar darajar kudin kasar da tsananin tsadar kayayyaki, sun kara hali na matsin rayuwa da kaso 82 cikin 100 a kasar. Sama da gidaje dubu 99 da kuma muhimman gine-ginen gwamnati gami da asibitoci yakin ya lalalata, an kuma yi kiyasin cewa kasar ta tafka asara a yakin na Isra'ila da Hezbollah da ta kai ta kimanin dala biliyan takwas da miliyan 500 koda yake wani bincike mai zaman kansa ya yi hasashen asarar na iya zarta dala biliyan 20. Yayin da duniya ke taimaka wa kasashen da yaki ya daidaita da biliyoyin kudi na tallafi, masana sun nunar da cewa sake gina Lebanon na bukatar dukiya mai yawan gaske. Kasar dai ba ta da shugaba tun cikin watan Oktobar 2022, bayan kammala wa'adin shugabancin tsohon shugaban kasa Michel Aoun. Majalisar dokokin kasar ta ce, za a gudanar da zaben shugaban kasa a ranar tara ga watan Janirun badi. Batun sake gina kasar batu ne da ya dogara da dorewar yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsakanin bangarorin da ke rikici wato Isra'ila da kungiyar Hezbollah, abin kuma da ke zaman babban fata da 'yan Lebanon ke da shi musamman a wannan lokaci.