1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaman lafiya ya fara samuwa a Laberiya

Yusuf Bala / LMJJune 30, 2016

Jami’an tsaro a kasar Laberiya za su karbi ayyukan tsaro, da dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya suka kwashe shekaru 13 suna gudanarwa a kasar da tai fama da yakin basasa.

https://p.dw.com/p/1JGs4
Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Laberiya, UNMIL
Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Laberiya, UNMILHoto: picture-alliance/dpa/K. Nietfeld

Sai dai ana ci gaba da samun fargabar cewa jami'an tsaro na cikin gida basu da kwarewar da za su iya gudanar da wannan aiki. Kididdigar bayanai a fannoni daban-daban na rayuwa da aka samu tun daga shekarar 2007 zuwa 2016 da muke ciki, na nunar da cewa ga dukkan alamu, a Laberiyan an samu ci gaba a wasu fannoni yayin da a wasu kuma lamuran sun kara tabarbarewa. Misali harkokin da suka shafi kare hakkin dan Adam da bin doka da oda an samu ci gaba idan aka kwatanta da lokutan baya da ma ayyukan ci-gaba ga al'umma ba wani ci-gaban a zo a gani, kana wadanda suka yi hijira daga matsugunansu na da yawan gaske. Za dai a iya cewa al'amuran tsaro sun inganta idan aka yi waiwaye daga shekarar 1989 zuwa ta 2003 inda aka rika samun dakarun sojan gwamnati da ‘yan tawaye da laifuka da suka hadar da kisan ban ji ba bangani ba, da yi wa mata fyade da sauran laifuffuka.

Jami'an 'yan sandan Laberiya
Jami'an 'yan sandan LaberiyaHoto: picture-alliance/ dpa/dpaweb

Shin ko dakarun kasar ta Laberiya sun shirya karbar wannan aiki? Waldemar Vrey shi ne mataimakin waikilin na musamman na Majalisar Dinkin Duniya a aikin wanzar da zaman lafiya karkashin rundinar UNMIL a Laberiya, ya kuma ce:

An samu ci gaba mai ma'ana

"Za a iya cewa ba komai ne aka samu ba dari bisa dari, amma da irin horon da muka bawa dakarun kasar tun daga shekarar 2003 kawo yanzu, za a iya cewa za su iya idan duka bangarorin na tsaro suka hada kai."

An rika janye dakarun na Majalisar Dinkin Duniya sannu a hankali, da fari yawansu ya kai 15,000 bayan yakin basasar kasar, sai dai kawo yanzu dakarun UNMIL din kasa da 4,000 ne kawai a Laberiya. Wasu dai ‘yan kasa irinus John Gweh mai shekaru 56 na mai ra'ayin ya kamata dakarun na Majalisar Dinkin Duniya, su ci gaba da kasancewa a kasar har abada duba da yadda ‘yan sandan kasa na LNP a wancan lokaci suka rika tirsasa jama'a tamkar dabbobi. To ko su wa za a ba wa harkokin gudanarwar ganin Amirka ta bada horo ga sojojin kasar yayin da ita kuma Majalisar Dinkin Duniyar ta maida hankali kan ‘yan sanda da sauran jami'an tsaro Vrey, ya ce sun mayar da hankulansu ne mafi akasari kan ‘yan sanda a Laberiya da jami'an lura da shige da fice inda suka sami horo kan yadda ya kamata su sa a bi doka da oda, a sabo da haka su ne za su karbi harkokin na tsaro tun daga daya ga watan Yuli mai zuwa.

Laberiya ta sha fama da cutar Ebola
Laberiya ta sha fama da cutar EbolaHoto: picture-alliance/AP Photo/Samaritan's Purse

Ebola ta taimaka wajen lalata kasar

Cutar Ebola dai ta kassara abubuwa da dama musamman harkokin tattalin arziki a wannan kasa, koda shi kansa shirin mika jan ragamar tsaron abin ya shafe shi, sai dai a cewar Vrey al'ummar kasar sun hada kai a yaki da wannan annoba kuma hakan zai taimaka su samar da sauyi a kasarsu. A kwai dai matsaloli irin na albashi da kayan aiki da 'yan sandan kasar ke fama da shi, yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke ware dalar Amirka miliyan 344 a duk shekara, karkashin shirin wanzar da zaman lafiyar na UNMIL. Laberiyan dai ta gabatar wa da majalisar dokokin kasar da bukatar kashe wa fannin na tsaro dalar Amirkan miliyan 90 daga wannan shekara ta 2016 zuwa ta 2017 a kasafin kudin bana inda a ke jiran amincewar majalisar.