Yaya makomar siyasar Faransa?
December 5, 2024Duk da cewa Emmanuel Macron zai yi jawabi ga al'ummar kasar domin bayyana alkiblar da Faransa za ta fusakanta, amma rikicin siyasa da na kasafin kudi da take fuskanta ya jefa ta cikin hali na rashin tabbas. Faduwar gwamnatin Michel Barnier mai ra'ayin jari-hujja ba ta zo wa 'yan Faransa da mamaki ba, duba da sarkakiyar da ke tattare da bakar gaba a tsakanin jam'iyyun da suka dare gida uku a majalisar dokokin kasar. Hasali ma dai, hada karfi wuri guda da jam'iyyun da ke da tsattauran ra'ayi irin su RN ta Marine Le Pen da LFI ta Jean Luc Melenchon suka yi ne ya ba su zarafin ganin bayan gwamnatinsa.
Karin Bayani: Shugaba Macron na rangadi a Afirka
Idan za a iya tunawa dai, rusa majalisar dokokin a watan Yuni da Macron ya yi ne ya sa jam'iyyarsa rasa kwarya-kwaryan rinjaye da take da shi a majalisa, inda maimakon haka jam'iyyun LFI da RN suka samu karfi fiye da shekarun baya. Pierre-Alexandre Anglade mamba na jam'iyyar Ensemble pour la République, ya zargi Marine Le Pen da Jean Luc Melenchon da zama kanwa uwar gami na halin da siyasar Faransa ta shiga. Kididdigar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar bayan kada kuri'ar yankan kauna ta nunar da cewa, kaso 53 cikin 100 na 'yan Faransa sun amince da matakin da majalisar ta dauka. Sai dai kuma a daya hannun kaso 82 cikin 100 na al'umma, na nuna damuwa game da makomar Faransa sakamakon kalubalen tattalin arzikin da ke gabanta.
Duk da kasancewarta kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a Turai, Faransa na fama da gibi a fannin ci-gaba baya ga bashin da ke neman yi mata katutu. Da ma dai Faransa na kashe Euro biliyan 60 a kowace shekara wajen biyan kudin ruwa na bashin da ake bin ta, kunshin kudin da ya zarta kasafin da ake ware wa fannin tsaro ko ilimi. Fadar shugaban Faransa ba ta sanar da lokaci da za ta nada sabon firaminista ba, amma Shugaba Macron zai yi jawabi ga 'yan kasa. Duk jam'iyyun siyasa da ke da wakilci a majalisar dokoki, ba su da rinjayen da zai ba su damar samun wannan matsayi kai tsaye.
Karin Bayani: Kasashe rainon Faransa na korar sojojinta
Maimakon haka ma dai, jam'iyyar La France Insoumise (LFI) mai tsattsauran ra'ayi, ta yi gargadin sake daukar matakin kayar da sabuwar gwamnati matukar dai ba a nada mai kwarya-kwaryar ra'ayin gurguzu ba. Tuni ma shugabar 'yan majalisan LFI Mathilde Panot ta bukaci Macron da ya yi murabus tare da shirya zaben wuri, domin a warware kiki-kika da ake ciki. Cibiyar Kimanta Tattalin Arziki ta Moody's ta kiyasta a cikin wata sanarwa cewa, faduwar gwamnati Faransa ta rage kimanta a cibiyoyin kudi na duniya tare da jefa ta cikin wadi na tsaka mai wuya a fannin siyasa. Wannan dai shi ne karo na biyu, cikin tarihin siyasar Faransa da aka kada kuri'ar yankan kauna ga gwamnati.