Taron zai maida hankali a kan yarjejeniyar MINSK
June 23, 2015Talla
Ministocin na waiwaye adon tafiya ne a game da inda aka kwana dangane da aiwatar da yarjejeniyar MINSK a Ukraine.Wannan saduwa dai na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da Ƙungiyar Tarrayar Turai,ta amince da wani ƙudirin tsawaita takunkumin karya tattalin arziki ga Rasha saboda rawar da take takawa a yaƙin da ake yi a gabashin Ukraine.
An dai ci gaba da gwabza yaƙi tsakanin dakarun gwamatin da na 'yan aware a gabashin ƙasar duk da yarjejeniyar tsagaita buɗe wutar da aka cimma a watanni huɗun da suka gabata.