Sojojin Faransa sun halaka dan IS a Nijar
December 21, 2021Talla
Sojojin Faransa sun sanar a wannan Talata cewa sun yi nasarar kashe daya daga cikin 'yan ta'addar IS da suka kai wa ma'aikatan agaji na Faransa da ke aiki a Jamhuriyar Nijar hari a shekarar da ta gabata.
Faransawan sun ce a ranar Litinin ne dai sojojin nasu hadin gwiwa da na Nijar suka bindige dan ta'addar a wani hari ta sama bayan da aka samu labarin cewa yana cikin wadanda suka halaka Faransawa a bara.
'Yan kungiyar ta IS dai sun halaka Faransawa shida da wasu 'yan Nijar biyu a lokacin da suka kai hari kan ma'aikatan agajin na Faransa a shekarar da ta wuce. A watan Agustar da ya gabata sojojin Faransan sun ce sun bindige jagoran mayakan IS da suka kitsa harin.