1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa ta nemi kawo karshen rikicin Gaza

July 13, 2014

Faransa ta nemi da a gaggauta kawo karshen rikicin da ke wakana tsakanin Isra'ila da kungiyar nan ta Hamas da ke Gaza.

https://p.dw.com/p/1Cc45
Palästina Israel Luftangriff auf den Gazastreifen 13.07.2014
Hoto: Reuters

Ministan harkokin wajen Faransa Lauren Fabius ne ya bayyana hakan a wannan Lahadin inda ya ce abin da ya kamata a yi yanzu shi ne a tsagaita wuta tare da yunkuri na sasanta bangarorin biyu.

Rahotanni da ke fitowa yanzu haka daga Gaza na cewar yawan wadanda suka hallaka sakamakon barin wutar da dakarun Isra'ila ke yi yanzu haka ya kai dari da sittin da takwas. Daga cikin wanda suka rasun a baya-bayan nan har da wasu mutane goma sha shidda daura da gidan kwamishinan 'yan sandan Hamas daidai lokacin da suke fitowa daga wani masallaci.

Har wa yau wasu karin mutane sama da dubu daya sun samu raunuka kamar yadda kakakin hukumar ba da agajin gaggawa ta Gaza Ashraf al-Qedra ya shaida wa manema labarai.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal