Faransa na son kungiyar NATO shiga yaki a yankin Sahel
November 28, 2019Talla
Emmanuel Macron ya fadi hakan ne yayin ganawar da suka yi da shugaban kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg a birnin Paris, inda ya ce yin hakan zai yi matukar tasiri ga dakile ayyukan na ta'addanci. Shugaban na Faransa ya kuma nemi batun ya kasance daya daga cikin manyan batutuwan da kungiyar za ta tattauna a babban taronta da za a gudanar a birnin Landon na Birtaniya nan gaba kadan.