Faransa: Za a kara tsaurara tsaro
July 16, 2016Talla
Kamfanin dillancin labarai na AP ya rawaito ministan cikin gidan Faransa din Bernard Cazeneuve na cewar karin 'yan sanda kimanin dubu 12 za su shiga aikin tabbatar da tsaro a kasar baya ga wasu soji da 'yan sanda kimanin dubu 120 da dama can ke yin wannan aiki.
Mr. Cazeneuve ya ce gwamnatin Francois Hollande ta yanke wannan shawarar ce da nufin ganin an tsaurara tsaro a kowanne loko da sako na kasar domin magance kai hari kan wanda ba su ji ba, ba su kuma gani ba.
A 'yan watannin nan Faransa ta fuskanci hare-hare na kunar bakin wanke wanda masu kaifin kishin addini da ke da alaka da IS suka kai a wurare daban-daban kuma hakan ya yi sanadin rasuwar mutane da dama.