Faransa za ta hana masallatai karbar agaji
July 29, 2016Talla
Gwamnatin kasar Faransa ta bayyana aniyar ta na dakile dukkanin agajin kudade da Masallatan kasar ke samu daga sauran kasashen duniya. Firaminstan kasar Manuel Valls ya ce ya na duba yiwuwar sauya wannan fasali zuwa wani sabon tsari na zamani da zai sabunta dangantar mabiya addinin Islama a kasar.
An kuma kirayi shugabannin addinan da su kauracewa daukar tsauraran akidu da suke koyowa a wasu kasashe. Wannan sabon mataki dai na zuwa ne bayan kasar Faransa ta fuskanci manyan hare-hare uku cikin watanni 18 da suka gabata wanda aka hakikance cewar 'yan kungiyar IS suka kaisu.