1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransanci na samun koma baya a Senegal

Salissou BoukariNovember 28, 2014

A daidai lokacin da kasashen masu amfani da harshen Faransanci ke taro a Dakar, harshen Faransanci na samun koma baya a gaban harshen Wolof na kasar ta Senegal.

https://p.dw.com/p/1DwlK
Frankophonie-Gipfel in Kinshasa
Hoto: dapd

A cikin kotu na Senegal, ko ma a kan tituna, kusan dukkanin huldodin 'yan kasar, ana yinsu ne cikin harshe su na gida Wolof. Saboda haka ne amfani da harshen Faransanci ke kara raguwa a kasar ta yammacin Afirka. A cewar farfesa Aliyu Ngone Seik malami a jami'ar Sheik Anta Diop da ke birnin Dakar " a nan Senegal Faransanci shi ne kan gaba wajae rubutu, amma kuma harshen Wolof shi ne kan gaba da ake magana da shi"

A 'yan shekarun da suka gabata, 'yan kasar ta Senegal sun shahara wajen lakantar wannan harshe na Faransanci. Sai dai a yanzu akasin haka ake fuskanta. Lamarin da ya ba wa Farfesa Aliyu Ngone Seik mamaki, ganin yadda lamari ya yadu a sassa daban-daban na kasar ta Senegal. Ya ce: " harshen faransanci na samun koma baya a ko'ina, har ma a cikin ma'aikatu na gwamnati kamar misali a Majalisar dokoki"

Yanzu dai 'yan kasar Senegal da dama, ba sa ma boye bukatarsu ta neman mayar da harshen Wolof harshen kasa. Wannan zai sanya Faransanci cikin tsaka mai wuya duk kuwa da cewa shi ne harshe na aiki a hukumance a wannan kasa.