1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fararen hula a Sudan ta Kudu na fuskantar karancin abinci

Suleiman BabayoAugust 1, 2015

Rufe hanyoyin kogin Nilu da mahukuntan kasar Sudan ta Kudu suka yi yana shafan aikin kungiyoyin ba da agaji na kasa da kasa.

https://p.dw.com/p/1G8OV
Symbolbild Frauen Opfer Konflikt Südsudan
Hoto: GetttyImages/AFP/C. Lomodon

Kungiyoyin ba da agaji a kasar Sudan ta Kudu sun ce dubban fararen hula na fuskatar karancin abinci, saboda mahukuntan kasar sun toshe hanyoyin da ke kai wa jihar Upper Nile, sakamakon rufe hanyoyin ruwa.

Ana amfani da hanyoyin kogin saboda matsalolin da ake da su kan tituna da kananan wuraren saukan jiragen sama. Sai dai wani kakakin sojin kasar ya ce an rufe hanyoyin kogin na wani lokaci, saboda 'yan tawaye suna amfani da damar ta hanyar kaddamar da hare-hare kan dakarun gwamnati.

Kasar ta Sudan ta Kudu da fada cikin yakin basasa lokacin da Shugaba Salva Kiir ya zargi tsohon mataimakinsa Riek Machar da yunkurin kifar da gwamnati.