Farashin danyen mai ya kara faduwa
April 18, 2016Kace nace da ke wanzu tsakanin Saudiyya da kuma kasar Iran na daga cikin irin batutuwan da suka yi sanadin rushewa tattaunawar da aka gudanar a birnin Doha na daular Qatar da nufin rage yawan man da ake tonowa saboda a daga farashinsa. Iran dai ta ki amincewa da batun rage man lamarin da ya sanya Saudiyya ta ce ita ma ba za ta rage nata ba.
Wannan yanayi da ya sanya faduwar farashin man a kasuwannin duniya da kashi 5 cikin 100 kuma ma wasu masu fashin baki kan cinikayyar man na ganin farashin zai iya yin kasa. 'Yan kasuwa da masana tattalin arziki a nasu bangaren na ganin wannan yanayi da ake ciki zai iya shafar tattalin arziki na duniya ta bangaren cigabansa duk kuwa da cewar an ci moriya daga karyewar farashin man da aka samu.
Tuni dai wannan lamari ya fara tada hankalin sauran kasashen da ke dogaro da mai wajen samun kudin shiga musamman ma ma wanda ke Afirka. Kasashen dai na ganin wannan halin da aka shiga zai iya fadada irin matsalar matsin tattalin arzikin da suke fuskanta sai dai Mahaman Lawan Gayya wanda jami'i a kungiyar kasashen Afirka masu hako man fetur ya ce kasahen Afirka na fafutuka wajen nemawa kansu mafita daga wannan matsala.
To yayin da kasashen na Afirka da ma saura sassan duniya da ke dogaro da danyen mai wajen samun kudaden shiga ke nuna fargaba kan wannan hali da ake ciki wadna ya sanyasu nemawa kai mafita, a share guda ministan makamashi na daular Qatar Salah Muhammad cewa ya yi akwai yiwuwara cimma matsaya a taron da kasashen na kungiyar ta OPEC sai dai wasu na ganin muddin Iran da Saudiyya ba su daidaita ba to da wuya a iya kaiwa ga ci.