1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Farashin fetur ya karye

Suleiman Babayo AH
March 10, 2020

Saudiyya ta bayyana shirin kara yawan man fetur da take kai wa zuwa kasashen duniya yayin da farashin danyen man fetur na kara karyewa a kasuwannin duniya.

https://p.dw.com/p/3Z9TB
Ölplattform
Hoto: picture-alliance/PA Wire/D. Lawson

Katafaren kamfanin man fetur na kasar Saudiyya da ake kira Saudi Aramco ya bayyana tsarin kara yawan man fetur da kasar ke fitarwa zuwa kasashen ketere daga farkon watan Afrilu mai zuwa zuwa ganga milyan 12.3 kowace rana, yayin da kamfanin ke kara fito-na-fito da kasar Rasha kan kudaden man fetur a kasuwar duniya.

Mahukuntan Saudiyya sun fusata saboda Rasha ta yi watsi da shirin da kasashen masu arzikin man fetur na kungiyar OPEC suka gabatar kan zabtare man fetur da ake kai wa kasuwannin duniya da ganga milyan 1 da rabi. Maimakon haka minsitan makamashi na Rasha, Alexander Novak, ya bayyana shirin kara yawan man fetur da kasarsa ke kai wa kasashen duniya daga ganga 500,000 kowace rana zuwa ganga milyan 1.7.

Wannan na zuwa yayin da farashin man fetur ya karye a kasuwannin duniya da kashi 25 cikin 100, inda farashin ya koma Dala 37 kan kowace gangar danyen man fetur.