1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar barkewar yakin basasa a Sudan ta Kudu

December 19, 2013

Dakarun dake biyayya da tsohon mataimakin shugaban Sudan ta Kudu sun yi fatali da shirin sulhu a rikicin kasar da kawo yanzu ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane.

https://p.dw.com/p/1AdgT
Hoto: Getty Images

'Yan tawayen Sudan ta Kudu dake fafatawa da dakarun gwamnati sun yi watsi da duk wani yunkuri na neman zaman lafiya a daidai lokacin da yankin ke kokarin hana wannan jaririyar kasa rushewa, shekaru biyu kacal bayan kirkiro da ita. Dakarun dake biyayya da tsohon mataimakin shugaban kasa Riek Machar sun kwace garin Bor da yammacin ranar Laraba yayin da fada kuma ke ci gaba a gabacin jihar Jonglei. Shugaba Salva Kiir ya dora alhakin tabarbarewar tsaron a kan wani yunkurin juyin mulki da tsohon mataimakinsa ya shirya. Sai dai Machar ya musanta wannan zargi. An kiyasta cewa mutane kimanin 450 aka kashe a birnin Juba tun bayan barkewar rikicin a ranar Lahadi da ta gabata. A halin da ake ciki manyan ministoci daga kasashe hudu na yankin da suka hada da Kenya, Djibouti, Habasha da kuma Yuganda sun isa Juba a kokarin kaddamar da wani yunkurin kawo zaman lafiya.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu