Fargabar komawar mayakan IS 6,000 zuwa Afrika
December 11, 2017A 'yan watannin nan ne dai rahotanni suka tabbatar da murkushe ayyukan kungiyar, musamman a kasashen Siriya da Iraq, inda masana harkokin tsaro da masu sharhi ke ganin ya kamata Afirika ta yi tanadi don wannan kalubale da za ta iya tsintar kai a ciki, kamar yadda Cummings Ryan wani masanin tsaro kuma mai yin sharhi da ke Cafe Town a Afirika ta kudu ya nunar.
Ita dai Kungiyar ta'adda ta IS mai da'awar kafa sabuwar daular Islama reshe ne na Kungiyar Al-Kaida a Iraki wacce ta bayyana a shekara ta 2013 daidai lokacin da ake gwabza yakin Siriya, inda ta yi nasarar hade kan kungiyoyi masu mabambantan akidoji da manufofi musamman daga kasashen Afirka da LarabawaSai dai a iya cewa karshen alewa dai kasa don kuwa tun daga lokacin da gwamnatin kasar Siriya ta samu goyon baya daga wasu kasashen yammacin Turai da kuma kasar Iran duniya ta fara ganin yiwuwar murkushe wannan kungiya.
Small Chergui shi ke zaman shugaban sashen zaman lafiya da tsaro na kungiyar tarayyar Afrika ya fidda wata sanarwa a birnin Aljiyas na kasar Aljeriya yayin wani taro cewar sama da 'yan Afirika 6,000 wadanda suka taimakawa ayyukan tarzomar kungiyar ta IS ake sa ran zasu koma kasashensu a halin yanzu kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar ya sanar.
To sai dai ita ma kungiyar tarayyar Afrika na hasashen komawar wadannan dakaru gida zai iya zama barazana ga zaman lafiyar yankin, a don haka ta ce akwai matukar bukatar hadin gwiwa da yin aiki tare a tsakanin kasashen Afrika don tunkarar bullar duk abin da zai kawo tashe tashen hankula a kasashen.
Ita dai wannan kungiyar ta'addanci ta IS da ma tafi kamari ne a kasashen Siriya da Iraki kafin daga baya ta fara fantsama bangare daban daban na duniya inda daga cikin kasashen da guguwar wannan kungiya taje har da wasu daga cikn kasashen Afrika,