Fargabar satar muhimman bayanan mutane
April 24, 2018A Najeriya ga misali a lokutan baya gwamnatoci sun matsa lamba wajen ganin any i wa layin waya rijista, inda mutane ke ba da bayanansu ciki har da na sirri, za ka kuma ka iya gani an sanya bayanan mutum cikin wata na'urar kwamfuta amma sai ka ga an sake siyar da ita ga wani mutum na daban wanda masu zamba kan iya amfani da wadannan bayanai. Wannan zai nuna maka yadda al'umma ke sanya bayanansu ko ina ciki kuwa har da shafukan sada zumunta. Hakan kuwa na zuwa lokacin da aka shiga muhawara kan satar bayanai na kamfanin Cambridge Analytica.
A makonni da suka gabata mujallar Guardian ta Birtaniya ta ba da rahoton cewa kamfanin Oligarch da ke zama uban gida ga Cambridge Analytica ya je Najeriya kafin zaben 2015 don yin kamfe na adawa da takarar Muhammadu Buhari ta hanyar tattara bayanai da suka shafi shugaban. Batun da gwamnatin Najeriya ta ce za ta duba a bangare guda kuma kamfanin yaki aminta da zargin.
Akwai dai mutane miliyan 177 da ke amfani da Facebook a Afirka da yawa na amfani da tsarin nan na "Free Basic" su tura bayanansu. Babban abin dubawar a Afirka shi ne mafi akasarin kayan da suka shafi sadarwar shigar masu da su kawai ake yi , misali tarho daga China ko samun wasu bayanai daga Amirka da kamfanonin sadarwa na Turai da sauransu, ba a hada wadannan kaya a Afirka don haka sai yadda kamfanoni na waje suka yi da 'yan Afirkar ta fuskar tunaninsu da ma kare masu bayanansu.
Akwai kuma 'yan Afirka wadanda suka yi ammannar cewar idan ba su da abin boyewa ba su ga wata matsala ba idan aka ga bayanansu. An dai dauki lokaci ana muhawara a mataki na Kungiyar Tarayar Afirka kan yadda za a tunkari matsalar kare bayanan da ma tsaro a intanet tun daga shekarar 2011 sai dai baya ga Senegal da ta tanadi hukuma da ke sa ido kan batun da dama daga kasashen na Afirka ba su yi wata doka ba.