1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

211209 Pakistan Taliban

December 21, 2009

Har yanzu sojojin Pakistan na ci-gaba da kai farmaki a yankin Waziristan, inda alamu ke nuni da cewa rundunar sojin Pakistan ta ƙuduri aniyar murƙushe abokan gaba na cikin gida.

https://p.dw.com/p/LAAH
Dakarun Pakistan dake kai farmaki kan TalibanHoto: AP

Hafsan hafsoshin sojin Amirka Michael Mullen wanda a kwanakin bayan nan ya kai ziyara birnin Islamabad ya bayyana farmakin da sojin Pakistan ke yi a Waziristan da cewa kwalliya na mayar da kuɗin sabulu.

"An yi wa abin shiri mai kyau, kuma ana aiwatar da shi yadda ya kamata."

Ba safai dai Amirka ke yabawa da aikin rundunar sojin Pakistan ba. Alal misali a farkon wannan shekara lokacin da hukumomin Pakistan a yankin Kwarin Swat suka ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya da ´yan Taliban sannan suka doshi babban birnin ƙasar, ƙasashen yamma sun nuna ɓacin ransu. To amma tun wannan lokaci abubuwa sun sauya. Da farko sojojin sun fatattaki ´yan takifen sannan yanzu sun kai yankunan ƙabilu. Shugaban gidauniyar Heinrich-Böll a birnin Lahore na Pakistan Gregor Enste ya bayyana farmakin da sojojin suka fara a cikin watan Oktoba kan ´yan Taliban a Kudancin Waziristan kamar haka.

"Wani gagarumin farmaki ne kuma a ƙarshe sojojin sun gane cewa suna fafatawa ne da abokan gaba na cikin gida amma daga waje ba. Lalle ana cikin mawuyacin hali."

Shi ma tsohon Janar kuma masani kan harkokin tsaro Talat Masood ya bayyana farmakin da cewa yayi nasara. Ya jaddada cewa rundunar sojin Pakistan suna rarrabewa sosai tsakanin ´yan Taliban da suke yaƙa.

"Pakistan dai tana abin ya zama wajibi ne akan ta amma ba don ta daɗaɗawa Amirka rai ba. A wani lokacin dai buƙatun su sun banbanta da juna, domin Pakistan ba zata iya ɗorawa kanta nauyin yaƙar Taliban na Afghanistan ba. Wannan aikin Amirka da ƙungiyar tsaro ta NATO ne."

Wani kyakyawan sauyi ne yadda sojojin ke rarrabewa tsakanin Taliban na Afghanistan da na Pakistan. Yanzu haka dai jama´a na goyon bayan farmakin da sojojin ke kaiwa duk da ƙoƙarin da ´yan Taliban ke yi na janyo hankalin jama´a ta hanyar kai hare hare a tsakiyar birane. ´Yan Taliban na masu ra´ayin cewa suka tsananta hare haren ƙunar baƙin wake a birane to watan-wata rana jama´a za su juwa sojoji baya bisa hujjar cewa saboda farmakin sojojin ne Taliban ta tsananta na ta hare hare. Saboda haka Gregor Enste na gidauniyar Heinrich-Böll ke da ra´yin cewa goyon bayan da ake bawa sojojin ba zai ɗore ba.

"Wannan yaƙin da ake yi da Taliban zai ɗauki shekaru kamar yadda muka gani a Sri Lanka. Idan da gaske al´umar Pakistan ke yi wajen goyawa sojojinsu baya to ya zama wajibi su kwana da sanin cewa za su shafe lokaci mais tsawo a ƙarƙashin wannan mummunar zubar da jini."

Tarihin Pakistan ya nuna cewa makomar ƙasar ta dogara kan sojojinta ba ma kawai ga ƙasar kaɗai ba a´a har da ma ƙasashen yamma.

Mawallafa: Kai Küstner/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Halima Balaraba Abbas