A kokarin karfafa al'adu da dangantaka a tsakanin Najeriya da Nijar, an bude wani kamfanin shirya fina-finan Hausa na bai daya mai suna: "Nijar Najeriya Film Production," wanda zai bai wa jarumai da mawakan kasashen biyu damar yin aiki tare. An gudanar da gagarumin bikin kaddamar da kamafanin, mai shalkwata a birnin Damagaram Na Jamhuriyar Nijar din.