1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Finland da Sweden sun mika bukatunsu ga NATO

Usman Shehu Usman AH
May 18, 2022

A hukumance kasashen Finland da Sweden suka mika takardun neman shiga kungiyar tsaro ta NATO, jakadun kasashen biyu a kungiyar ta NATO ne, suka mika takardunsu ga sakatare janar na kungiyar Jens Stoltenberg.

https://p.dw.com/p/4BTN7
 Daga hagu zuwa dama Klaus Korhonen jakadan Finland a NATO,Sakatare-Janar na NATO Jens Stoltenberg da Axel Wernhof jakadan Sweden a NATO
Daga hagu zuwa dama Klaus Korhonen jakadan Finland a NATO,Sakatare-Janar na NATO Jens Stoltenberg da Axel Wernhof jakadan Sweden a NATOHoto: JOHANNA GERON/AFP

Dama dai tun bayan da kasar Rasha ta kaddamar da yaki kan kasar Ukraine sauran makobtan Rasha da ba sa cikin NATO suka fara rudewa kan abin da ka iya faruwa da su, kuma shugabannin NATO suka fara kiran wadannan manyan kasashen yankin Balkan da su fara tunanin shiga NATO. Da yake karban takardun Sweden da Finland, sakatare janar na kungiyar ta NATO Jens Stoltenberg ya ce nan da kwanaki talatin dole a kammala tattauna batun shigan kasashen biyu wanda mambobi 30 na kungiyar za su yi. Ya kwatanta ranar ta yau a matsayin ranar murna:

"Yau kyakkyawar rana ce a cikin mayuwacin halin tsaro da muke fama da shi. Ina yi muku matukar godiya bisa mika takardun neman shiga NATO. Ko wace kasa na da 'yancin zabar inda za ta yi kawance. Dukkaninku biyu kun yi zabinku bayan kyakkyawar bin tsarin dimukaradiyya. Ina gagarumin maraba da bukatar Finland da Sweden na hadewa da NATO".

Akalla dai za a dauki makwanni biyu kafin mambobin NATO su kammala mahawara bisa bukatar kasashen biyu na shiga kungiyar ta NATO.

Turkiyya na nuna adawa da shigar kasashen biyu a cikin  NATO

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan
Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip ErdoganHoto: Turkish Presidency/AP/picture alliance

Sai dai kuma tuni shugaban kasar Turkiyya Raccep Tayyip Erdogan ya nuna matukar damuwarsa kan shigar da kasashen na Sweden da Finland cikin NATO, inda ya bayyana korafin da kasar ke da shi kan kasashen.

"Mun nemi Sweden ta mika mana 'yan ta'adda 30 da ke kasar, a taso mana keyarsu gida, amma kuka ce ba za ku yi ba. Ka ki ba mu 'yan ta'adda, amma yanzu kuma kana son mu kyale ku ku shiga kungiyar NATO. NATO kungiya ce ta tsaro. Hukuma ce ta tsaro. Don haka ba za mu yarda da shigar da ku a wannan kungiya ba."

Wasu kasashen Turai na murna da bukatar kasashen na Finland da Sweden

Flagge der NATO sowie von Schweden und Finnland
Hoto: Jakub Porzycki/NurPhoto/picture alliance

Shugaban kasar ta Turkiyya ya yi jawabin nasa ne sa'o'i bayan da kasashen Sweden da Finland suka mika takardun neman shiga NATO, inda Erdogan ke zargin kasashen biyu da mara baya wa kungiyar Kurdawa ta PKK ,wacce Turkiyya ke daukar mai aikata ta'addanci.

Sai dai shi kuwa Firaministan Italiya Mario Draghi cikin murna ya karbi bukatar da kasashen biyu suka gabatar:

"Bukatarsu ta shiga NATO babban martani ne ga mamayar Ukraine da Rasha ta yi da kuma barazanar da hakan yake yi wa tsaron Turai. Italiya ta goyi bayan yanke hukuncin da Finland da Sweden suka yi na neman zama mamba a NATO".

Tuni dai manyan kasashen kungiyar ta NATO kamar su Jamus, Amirka, Faransa da Birtaniya duk suka yi marhabin da jin cewa kasashen biyu na son shiga NATO, wannan kuwa tun ma kafin Finland da Sweden su sanar a hukumance bukatar shiga kungiyar. Ita ma Rasha wacce kusan don ita wadannan kasashen biyu suka nemi shiga NATO, ta bayyana cewar shigar kasashen a kungiyar ba zai kasance ba tare da martanin daga gareta ba. Kasashen na Finland da Sweden suna iyaka da Rasha, yayin da Finland ke iyaka da Rasha mai fadin gaske ta kasa, ita kuwa Sweden tana iyaka da Rasha ne ta ruwa.