Yunkurin halaka firaiministan Isra'ila
April 28, 2022Talla
Rahotannin sun tabbatar da shirin halaka iyalan Firaiminista Naftali Bennett da yanzu haka ke fuskantar barazanar kisa daga wasu da ba a iya tantancewa ba, rundunar tsaron kasar ta sheda hakan ne, bayan da aka tura masa wata wasika da aka sanya harsashin bindiga a ciki. Masu binciken sirri na zargin cewa, dan Firaiministan mai shekaru goma sha bakwai ake hari a baya-bayan nan.
Daga bisani ne Firaiminista Naftali ya fito ya gargadi 'yan kasar a game da munmunan tasirin da kasa ka iya fadawa ciki a sakamakon rarrabuwar kawuna, a lokacin da yake jawabi ga 'yan kasa a taron tuni da kisan kiyashin da aka yi wa Yahudawa.