SiyasaJamus
Firaministan Isra'ila ya yi ikirarin lashe zabe
March 24, 2021Talla
Firaminista Benjamin Netanyahu, wanda ya fi kowa dadewa a wannan matsayi a tarihin Isra'ila, ya yi fatan zaben zai ba shi damar kafa gwamnati ba tare da wata hadakar ba, abin da ake ganin da wuya ne ya cimma hakan.
Kuri'ar jin ra'ayi dai ta nuna yiwuwar jami'iyyar Mr. Netanyahun ta samu 'yar galaba a majalisar.
Cikin watan Disambar bara ne gwamnatin ta wargaje sakamakon rashin jituwa tsakanin Mr. Netanyahu da madugun adawa Benny Gantz da suka yi hadin gwiwa wajen kafa ta.
Firaminista Netanyahu wanda ke fama da zarge-zarge ciki har da na cin hanci, ya yi tutiyar cin zaben saboda kokarin da ya yi a bangaren yaki da cutar corona.