1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Libya: Sarraj zai yi murabus don zaman lafiya

Abdullahi Tanko Bala
September 17, 2020

Shugaban gwamnatin Libya da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita yace yana shirin sauka daga karagar mulki nan da makonni shida a wani yunkuri na cimma yarjejeniyar zaman lafiya.

https://p.dw.com/p/3iaoB
Fayez al-Sarraj
Hoto: picture-alliance/ZUMAPRESS/PPI

Libya ta sha fama da tashin hankali kusan shekaru goma tun bayan tarzomar da ta sami goyon bayan kungiyar kawancen tsaro ta NATO a 2011 da ta kai ga kashe tsohon shugaban kasar Moamer Gaddafi

Firaminista Fayez al Sarraj shugaban gwamnatin hadin kan kasar na fuskantar adawa a gabashin kasar karkashin jagorancin Khalifa Haftar wanda yanzu aka kawo karshen farmakin da ya rika kai wa gwamnatin a birnin Tripoli.

Bangarorin biyu sun gana inda suka gudanar da tattaunawa a Moroco a watan da ya gabata inda suka sanar da tsagaita wuta da kuma alkawarin gudanar da zabe.