1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai wa firaminisata hari a Sudan

March 9, 2020

Rahotanni daga Khartoum fadar gwamnatin Sudan na cewa firaminista Abdalla Hamdok ya tsallake rijiya da baya a wani hari da aka kai ma tawagarsa.

https://p.dw.com/p/3Z6Ze
Abdalla Hamdok
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Lamarin ya faru a lokacin da firaministan  Abdalla Hamdok ya fito da tawagarsa don zuwa ofis. Bayan faruwar lamarin firaministan ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa ''ina cikin koshin lafiya kuma ina wurin da babu wani zullumi''. Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin harin. Sai dai firaminisatan ya ce wannan ba zai sanyaya masa gwiwa a yunkurinsa na kawo sauyi a kasar ba. Abdalla Hamdok dai ya hau mulki bayan rikicin shugabancin da ya biyo bayan hambarar da gwamnatin Omar Al-Bashir. A yanzu shi ne ke jagorantar gwamnatin hadin kan kasa wace ta kunshi sojoji da fararen hula.