SiyasaAfirka
Sudan: Firaminista Hamdok ya yi murabus
January 3, 2022Talla
Firaministan Sudan Abdalla Hamdok ya yi murabus daga mukaminsa a daidai lokacin da rikicin siyasa da zanga-zangar adawa da sojoji ke kara kamari a kasar.
''A bisa wadannan hujjoji dana bayyana, na yanke shawarar yin murabus domin bai wa wani ko wata damar jagorantar kasar zuwa salon mulkin dimukuradiyya.'' inji Hamdok
Sai dai Hamdok ya yi gargadin cewa halin da kasar ke ciki abu ne mai matukar hatsari ga makomarta. Tun dai dawo da shi mukaminsa a watan Nuwamba da sojoji suka yi bayan juyin mulkin watan Oktobar 2021, Abdalla Hamdok bai bayyana sunayen ministoci ba, lamarin da ya jefa Sudan cikin rashin tabbas.