1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Firamnistan Isra'ila ya yi jawabi wa majalisar Amirka

Suleiman BabayoMarch 3, 2015

Firamnistan Benjamin Netanyahu Isra'ila ya yi jawabi wa majalisar dokokin Amirka.

https://p.dw.com/p/1EkXh
USA Washington Rede Benjamin Netanjahu Kongress
Hoto: Reuters/G. Cameron

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya nemi ganin daukan matakan tabbatar da hana kasar Iran samun makamun nukiliya, a matsayin mataki guda a kan duk wata tattaunawa da Iran. Ya ce yanzu ne lokaci matsa kaimi kan Iran, saboda gwamnatin ba ta da wani banbanci da sauran tsageru masu kaifin kishin Islama. Kuma kasar tana cikin masu goyon bayan ayyukan ta'addanci.

Wannan jawabi yana zuwa makonni biyu kafin zaben Isra'ila da Firaminista Netanyahu yake neman wani sabon wa'adi na mulki.