Fiye da mutane 100 ne sun hallaka a Afghanistan
April 22, 2017Mahukunta a kasar Afghanistan sun bayyana cewar adadin mutane da suka rasu sakamakon hari a sansanin soja a Arewacin kasar a ranar Juma'a kawowa yanzu ya yi sanadi na rayukan sama da mutane100 baya ga wadanda suka sami raunika.Janar Daulat Waziri, da ke magana da yawun ma'aikatar tsaro a Afghanistan ya bayyana cewa harin na ranar Juma'a a sansani na 209 ya yi sanadi na rayukan gwamman sojoji baya ga wadanda suka samu raunika. Da fari dai ma'aikatar tsaro ta bayyana cewa sojoji 11 ne suka rasu baya ga wadanda suka samu raunika. 'Yan ta'addar dai sun je masallacin Juma'a ne da ke sansanin sojojin inda a nan suka tashi jigidar bama-bamai da ke daure jikinsu. A cewar Janar Waziri maharan su goma ne biyu ne suka tashi bama-baman yayin da sauran jami'an tsaro suka aikasu lahira bayan musayar wuta. Tuni dai kungiyar Taliban ta dauki alhaki na kai harin.