Fursunoni 1,500 sun tsere daga gidan yarin birnin Maputo
December 26, 2024Akalla fursunoni 1,500 sun tsere daga babban gidan yari da ke Maputo babban birnin Mozambik, a daidai lokacin da aka shiga rana ta uku na tashe-tashen hankula da suka barke bayan tabbatar da nasarar jam'iyyar Frelimo a zaben shugaban kasa. Sai dai a yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a ranar Laraba da maraice, sufeto janar na 'yan sandan Mozambik Bernardino Rafael, ya ce an kashe 33 daga cikin fursunonin da suka arce yayin da 15 suka jikkata a rikicin da ya gudana da ma'aikatan gidan yarin. Amma dai ya ce an yi nasarar kama fursunoni 150 daga cikin wadanda suka tsere.
Karin bayani: 'Yan adawa sun yi zargin tafka magudi a zaben kasar Mozambik
A jiya Laraba ne wasu gungun masu zanga-zangar kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa suka tinkari babban gidan yarin Maputo, lamarin da ya haifar da rudani da hayaniya da suka kai fursunonin ga fasa wata katangar domin tserewa. Sufeto Janar na ‘yan sandan ya nuna fargabar karuwar manyan laifuka, lamarin da ka iya ta'azzara rashin tsaro a cikin kwanaki masu zuwa a Mozambik. Dama dai fursunoni 30 da suka tsere na da alaka da kungiyoyin da ke ikirarin jihadi wadanda suka shafe shekaru bakwai suna ta'addanci a lardin Cabo Delgado da ke arewacin kasar.