HRW: Fursunoni na wahala a Iraki
July 4, 2019Talla
A cewar kungiyar Human Rights Watch dubban mutane da ke tsare a yawancin kurkuku na cikin hatsarin kamuwa da cututtuka sakamakon rashin tsabta.
Kungiyar ta ce akwai hotunan da ke nuna munin yanayin rayuwa da fursunonin ke ciki a gidajen yarin kasar, ciki har da gidajen gyara halinka na kananan yara da mata ke tsare.
Gwamnatin Bagadaza ta yi ikirarin karya lagon mayakan IS a shekarar 2017 kuma yawancin fursunonin da ke kulle a gidajen kason kasar mayakan IS ne da ake zargi da ayyukan ta'addanci.