1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fushin 'yan Afghanistan kan Amirka saboda hoton bidiyo

January 13, 2012

Wani hoton bidiyo da ya fito, cikin sa an ga yadda sojojin Amirka suka riƙa fitsari kan gawarwakin 'yan Afghanistan waɗanda kuma ake zaton 'yan Taliban ne da suka kashe a ƙasar.

https://p.dw.com/p/13jBs
U.S. Marines with NATO forces patrol in a deserted market of Marjah, Afghanistan, Wednesday, Feb. 17, 2010 (AP Photo/Altaf Qadri)
Sojan kundunbalan Amirka a AfghanistanHoto: AP

Wannan hoto na bidiyo ya jawo fushi mai yawa da matuƙar baƙin ciki tsakanin 'yan Afghanistan, dake kira ga sojojin Amirka su fice daga ƙasar su saboda sun ci mutuncin addinin musulunci, sun kuma ɓata sunan 'yan Afghanistan.

'Yan Afghanistan da suka ga hoton na bidiyo, dake nuna yadda sojojin Amirka suke cin mutuncin gawarwakin 'yan ƙasar ta hanyar yi masu fitsari, sun baiyana matukar fushi da bacin ransu, musamman saboda al'ummar Afghanistan musulmi ne, kuma addiin musulunci ya tanadi girmamawa ga mamaci, kuma babu wani addini ko al'ada da ta baiwa wani damar cin mutuncin gawa, kamar yadda sojojin na Amirka suka yi yanzu a Afghanistan. Saboda haka ne Abdul Malik, wani mazaunin Kundus yace sojojin Amirka da suka aikata wannan mummunan cin mutuncin ga yan kasar ta Afganistan tilas ne ayi masu hukunci mai tsanani.

"Yace babu wani addini, babu wata al'ada da ta bada damar wani ya lalata, ko yaci mutuncin gawa. Hatta gawar abokin gaba takan cancanci a mutunta ta. Wadanda suka aikata wannan laifi wajibi ne a hukunta su, hukunci mai tsanani yadda za su gane abin da suka yi ba daidai bane."

Shugaban Afghanistan, Hamid Karsai ya nemi Amirka ta ɗauki mataki na farko, kan waɗanda suka aikata wannan laifi, inda yace tilas a bincika wannan mummunan al'amari, wadanda suka aikata hakan a kai su gaban kotu. A wata 'yar gajeruwar sanarwa da ofishin shugaban ya bayar, Hamid Karsai yace gwamnnatin sa ta kadu matuka, ta kuma ji zafi mai yawa tattare da wannan hoto na bidiyo, dake nuna sojojin Amerika suna fitsari kan gawarwakin yan Afghanistan ukku. Rahotannin kafofin yada labarai na Amirka sun nuna cewar rundunar sojan kasar tuni ta fara bincike game da wannan abin kunya.

Berlin/ Der Praesident von Afghanistan, Hamid Karsai, verfolgt am Dienstag (06.12.11) im Bundeskanzleramt in Berlin waehrend einer Pressekonferenz die Fragen der Journalisten. (zu dapd-Text)
Shugaban kasar Afghanistan Hamid KarsaiHoto: dapd

'Yan Afghanistan da dama tuni sun fara kira ga gwamnatin kasar su ta tilasta janyewar sojojin Amirka daga kasar su. Da yawa suna ganin wannan hoto na Video ya jawo bata sunan Amirka a kasar, zai kuma haddasa gurbacewar dangantaka tsakanin ƙasashen biyu. Wani dan Afghanistgan dake baiyana fushin sa yace:

"Sojojin Amirka sun yi fitsari kan gawarwakin musulmi, saboda haka sun aikata babban laifi. Tun da kuwa sun yi hakan, basu da sauran abinda zai sanya su ci gaba da zama a kasar mu. Bama son mu kara ganin sojojin ketare a nan, tilas ne duk su fita."

Samun wannan abin kunya na Video a yanzu, kamar yadda masana suke gani, zai kawo cikas a kokarin da gwamnatin Afghanistan take yi na shawarwarin sulhu tsakanin ta da yan kungiyar Taliban. Tswon shekaru biyu kenan gwmanati a Kabul take kokarin ganin kungiyar ta Taliban ta zauna kan teburin shawarwari na hakika domin neman sulhu, sai dai yan tawayen suka ce basu zauna ga neman sulhu da gwamnati a karkashin shugaban kasa Hamid Karsai ba, ko da shike a baya-bayan nan, wani bangare na shugabannin kungiyar sun baiyana shirin su na samun kusanta tsakanin bangarorin biyu, inda ma har ake cewar Taliban din zata bude ofishin ta na farko na huldodi a daular Qatar. To sai dai wani masanin siyasa na Afghanistan, Sayfuddin Sayhoon yace:

Taliban soldiers with guns stand guard in Bamiyan, Afghanistan, in this undated but recent photo. Opposition leaders claimed Tuesday, June 5, 2001 at least 100 Taliban fighters died in the fighting Monday and Tuesday and that their soldiers had captured the strategic Yakawlang district in central Bamiyan province. The Taliban Islamic militia controls 95 percent of the country and is fighting the opposition to capture the remaining five percent. (AP Photo/Amir Shah)
Yan kungiyar Taliban a AfghanistanHoto: AP

"A ra'ayin na, masu adawa da sulhu a Afghjanistan ne a yanzu, suka bankado wannan abin kunya na hoton Video, domin hana kunsantar juna tsakanin Amirka da kungiyar Taliban."

Rundunar haɗin gwiwa ta ƙasashen yamma dake Afghanistan, wato ISAF, ta yi Allah wadai da waannan hoto na bidiyo, yayin da a sharhin ta na farko, ƙungiyar Taliban ta ce bata yi mamakin wannan hoto ba, ta kuma kwatanta Amirka a matsayin shaiɗan.

Mawallafa: Ratbil Shamel / Umaru Aliyu
Edita: Yahouza Sadissou Madobi