SiyasaJamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango
Shugaba Tshisekedi zai sha rantsuwar tazarcewa kan mulki
January 20, 2024Talla
Za a rantsar da Shugaba Félix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, bayan da kotun kolin kasar ta tabbatar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar mai cike da cece-kuce.
Ana dakon halartar manyan baki daga ciki da wajen Kwangon a bikin, da ke zama irinsa na biyu a tarihin rayuwar Félix Tshisekedi mai shekaru 60 a duniya. Masu hamayya da suka hada da Moïse Katumbi da Martin Fayulu da suka sha kaye a zaben, na ci gaba da fatali da sakamakon zaben, inda suka yi kira ga magoya bayansu da su fito zanga-zanga.